Spaghetti mai nikakken nama

#jumaakadai 'yar uwa kina canja salon girkinki ko kuwa kullum iri daya kike yi? Idan haka ne, matso kusa ki canja recipe na dafa taliya.
Spaghetti mai nikakken nama
#jumaakadai 'yar uwa kina canja salon girkinki ko kuwa kullum iri daya kike yi? Idan haka ne, matso kusa ki canja recipe na dafa taliya.
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki yi per boiling taliya ki ajiye a gefe
- 2
Sai ki zuba mai a pan, ki dauko nikakken namanki ki zuba a ciki, ki sa albasa, seasonings, ginger and garlic, curry da attarugu. Ki yi ta juya su har sai naman ya fara fiddo ruwa alamun ya fara dahuwa kenan
- 3
Sai ki zuba yankakken tumatur ki ci gaba da juyawa har sai kin tabbatar duk sun yi, ruwan naman ya fara tsanewa.
- 4
Ki dauki taliyar nan ki zuba a ciki, ki dan yayyafa ruwa kadan ba da yawa ba sannan ki rage wuta. Ki bar shi su karasa dahuwa kamar minti bakwai.
- 5
Enjoy
- 6
Keywords
Similar Recipes
More Recipes









sharhai