Dankalin hausa da sauce

Amcee's Kitchen @Amina69
Duba fa yanzu lokacin dankalin hausa ko ina kaje zaka ganshi kuma ga Kara lafiya ga dadi
Dankalin hausa da sauce
Duba fa yanzu lokacin dankalin hausa ko ina kaje zaka ganshi kuma ga Kara lafiya ga dadi
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki fere dankali Sai ki wanke ki tsane ruwan Sai kisa gishiri ki soya
- 2
Zaki wanke tarugu da tattasai ki daka
- 3
Sai ki wanke albasa ki yanka ta tsaye
- 4
Zaki samu tukunya kisa oil dan kadan Sai kisa albasa ki soya sama sama
- 5
Sai kisa citta da tafarnuwa da kika daka kisa kayan miya da kika daka, Maggie da duk spices din da kike dashi da black pepper
- 6
Idan ya soyu Sai kisa ruwa dan kadan Sai ki dauko dankalin ki zuba a tukunyan ki juya sosai Sai ki zuba kuci lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16651642




sharhai (2)