Miyan taushe

Wannan miya nayishi saboda challenge ne saboda inata tunani me nake dashi wanda ya dade a fridge Sai na tuna inada nikakken kayan miya a freezer yafi 1 month nace bari nayi amfani dashi a challenge hmmm wannan miya duniya ne #OMN

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki gyara tumatir, tarugu, albasa da tattasai,citta da tafarnuwa
Sai ki wanke ki jajjaga
Ki samu tukunya ki daura akan wuta Sai kisa manja da albasa ki soya Sai ki zuba kayan miyan ki - 2
Ki barshi ruwan ya tsotse Sai ki soya idan yayi Sai kisa ruwa kisa kayan kamshi,Magi da gyada
Zaki gyara gyadan ki daka yayi laushi - 3
Idan gyadan ya nuna Sai kisa lawashi da nama
Nidai nayi amfani da naman kaza bayan minti biyar Sai kisa alayyaho ki barshi yayi kaman minti biyu Sai ki sauke - 4
NOTE
Idan zaki wanke alayyaho zakisa gishiri kadan Sai ki wanke sosai sannan ki yanka
Ni ina wanke alayyaho kafin na yanka saboda idan akwai datti ko tsutsa karna yanka dashi - 5
Aci miyan taushe lafiya naci nawa da tuwan shinkafa
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai