Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki surfa ayarki sai ki wanke ki jiqa
- 2
Ki bare dabino ki wanke ki jiqa tareda kanunfari da fennel da Cardamom
- 3
Sai ki fasa kwakwanki ki juye ruwan Sanna ki fere bayan, ki wanke cucumber ki fere bayan shima duk ki aje gefe
- 4
Sai ki fere dankalinki ki yanka qanana yanda zaiyi saurin nuquwa tare da cucumber da dankalin kwakwa
- 5
Sai ki qare wanke ayarki idan ta jiqa tas ki kankare ginger kisa
- 6
Ki hada komi a waje daya ki niqa
- 7
Idan kika niqa sai ki dan qara ruwa kadan sai ki tace da qyalle mai kyau, idan kika tace sai ki juye madarar nan gwangwani daya ki juya kisa a fridge yayi sanya kou kisa qanqara
- 8
Idan kina buqatan zaki zaki iya sa sugar amma ni zaqin Ayan da dabinon ya ishe ni
- 9
Asha dadi lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16688227















sharhai (2)