Miyar wake da alyyaho 🍽

Zainab’s kitchen❤️
Zainab’s kitchen❤️ @ummu_aish
Bauchi Nigeria

Na dade ina so nayi miyar wake ban samu nayi ba. Sai da wannan challenge din yazo na (mu sarrafa wake hutun nan)sai na samu damar yi😊🙏 Alhamdulillah!

Miyar wake da alyyaho 🍽

Na dade ina so nayi miyar wake ban samu nayi ba. Sai da wannan challenge din yazo na (mu sarrafa wake hutun nan)sai na samu damar yi😊🙏 Alhamdulillah!

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1 hour
6 yawan abinchi
  1. 3Wake kofi
  2. Manja serving spoon 3
  3. Alayyaho dai dai buqata
  4. Attaruhu 5 kanana
  5. Tattasai 5 matsakaita
  6. Albasa 2 madaidaita
  7. 3Cittta guda
  8. guda 5 Tafarnuwa
  9. 1Ruwan kanwa cokali
  10. Gishiri cokali2
  11. Kayan dandano
  12. Kifi ko nama

Umarnin dafa abinci

1 hour
  1. 1

    Da farko na sirfa wake na. Na jiqa wake da ruwa na tsawon minti 7.

  2. 2

    Sai na tsane ruwan na zuba waken a turmi na daddaka shi kadan ba yanda ze fashe ba, yanda fatar zata salube ta bar waken sai na juye cikin roba nayi ta wanke wa ina tsane shi a cikin makwarari ina tsince fatar.

  3. 3

    Sai na diga kanwa na rufe yacigaba da dahuwa har saida ya nuna yayi luguf. Amfanin kanwa a wake shine yasa ya nuna da wuri. Sai na kawo whisk na farfasa wake Zaki iya using masher Kiyi mashing dinsa ya farfashe.

  4. 4

    Nayi ta wanke wa ina tsane ruwan ina tsince fatar har saida na tsince tas.Zaki iya sirfawa a blender idan blender ki nada kyau. Daga sai na zuba ruwa na dora waken a wuta. Daya fara tafasowa yana dahuwa

  5. 5

    Na
    Zuba na gauraya sosai. Na rufe ya Kara dafuwa yayi kauri sai na kawo yankakken alayyaho na zuba. Wasu suna yinta haka ba alayyaho Amma ni inasonta da ganye Shiyasa na saka. Zaki iya yi ba tare dashi ba.

  6. 6

    Na hada miyar ne da tuwon shinkafa Amma zaki iya cinta da semo, masara da sauran su. Aci dadi lafiya!🍽😀😋🌶

  7. 7

    Saina sauqe na dora wata tukunyar na zuba Markaden kayan miya na soya da manja sai na juye dafaffen waken nan akai na kawo gishiri da kayan dandano na zuba. Na kawo jajjen attaruhu, tattasai, albasa, tafarnuwa da cittta

  8. 8

    Daga kar she na kawo soyayyen kifi na na zuba akai na gauraya na rufe da marfi na wasu mintina a akan wuta kadan sai na kashe. Ban samu na dauki hoton miyar tare da tuwon ba😅 kai na yayi zafi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Zainab’s kitchen❤️
rannar
Bauchi Nigeria
Welcome 🤗 to my world 🌍 Glad to be with you on this journey 🚞Don’t shy away to go through all my recipes. Feel free to search & try any recipe of your choice. follow, like and comment❤️ lastly Don’t forget to give a feedback or cooksnap! Enjoy Surfing 🏄‍♀️ down my page. A little prayer or a word of encouragement will go a long way😇 thank you!🙏
Kara karantawa

sharhai (2)

Similar Recipes