Alkubus din Alkama da fulawa da yogurt akofi
Kitanadi miyan taushenki
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko Zaki tanadi wannan kayan da na lussafa
- 2
Sannan ki kwaba fulawa da ruwa da yis da sugar da gishiri da Mai da baking powder ko bakinsoda in baking soda ne kadan zakisa
- 3
Sannan kaman kwabin fanke zakiyi ki barshi yatashi kaman Rabin awa indai yis dinki yanada kyau
- 4
Sannan kishafe kofufukanki da Mai sannan ki dako kwabinki Wanda yayi ki ajiye waje guda
- 5
Sannan kisa yogurt kijuya
- 6
Sannan kizuba a kwabin Alkubus din acikin kufin
- 7
Sannan kijera Atukunyar danbunki kisa leda kirufe sannan kisa ruwa atunyar kasan sannan ki kunna wuta ki aza sannan ki aza tukunyar Saman kirufe ki bari yaturaru na minti Sha biyar
- 8
Sannan kifidda
- 9
Sannan ki fidda daga kufin
- 10
Sannan ki yanka yadda kike bukata Dama kin tanadi miyanki nataushe ko miyan ganye ko shirba zuba aci lafiya
- 11
Allah ya amintar da hannayenmu nagode
Keywords
Similar Recipes
More Recipes













sharhai (2)