Umarnin dafa abinci
- 1
Agyara waken soya a wqnke a markada sannan a tace da abin tata sai a zuba ruwan a tukunya a dora a wuta abarshi ya tafasa sai a zuba ruwan tsami zaaga ta dunkule gu daya sai a juye a abin tata a kulle ruwan ya fita sai a kunce a yanka yadda ake so sai a tsoma cikin jikakken farin maggi sannan a soyasu a mai
- 2
Idan an gama zaa wanke attaruhu da albasa a jajjagasu sai a zuba mai kadan a kasco a soya sama sama sai a sauke a zuba awarar a ciki a cakuda
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8269024



sharhai