Kosan cous cous

Amcee's Kitchen
Amcee's Kitchen @Amina69
Zaria,kaduna State

Gaskiya ban cika son cous cous ba saboda idan nayi yana chabewa amma idan naje wani gurin ima cin ,amma aunty na ta koya min yanda ake kosan cous cous kuma da naci naji dadi saosai kuma ya kamata Ku gwada zakuji dadi#kosaicontest

Kosan cous cous

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

Gaskiya ban cika son cous cous ba saboda idan nayi yana chabewa amma idan naje wani gurin ima cin ,amma aunty na ta koya min yanda ake kosan cous cous kuma da naci naji dadi saosai kuma ya kamata Ku gwada zakuji dadi#kosaicontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Cous cous Kofi daya
  2. Tattasai guda hudu
  3. Albasa rabi
  4. Magi guda biyu
  5. Kwai guda daya
  6. Ruwan dumi kwatan Kofi
  7. Mangyada na soya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga kayan da ake bukata amma ban dauki ruwan dumi ba

  2. 2

    Zaki samu kwano kisa cous cous da ruwan dumi amma kar kisa ruwan duka sai ki barshi yayi minti uku

  3. 3

    Kafin lokacin yayi sai ki gyara tattasai da albasa ki wanke kiyi giretin dinshi sai kisa acikin cous cous din kisa magi da kwai

  4. 4

    Zaki ta juyawa har na minti biyu saboda su hade jikin su idan kin gama sai kisa mangyada akan wuta inyayi zafi sai ki wanke hannunki ki rinka iba da hannu kina sawa acikin mangyadan idan yayi ja sai ki juya dayan gurin yayi inshima yayi sai ki kwashe kisa a abin tsama saboda mai ya tsane acid lfy zaki iya ci da tea ko kunu

  5. 5

    Sai kisa yaji kici dashi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Amcee's Kitchen
rannar
Zaria,kaduna State
cooking is my fav
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes