Soyayyen dankali da kwai

abubakaraishatu @cook_13841005
Soyayyen dankali da kwai
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fere dankalinki ki yankashi a tsai-tsaye ki wanke kisa gishiri kadan
- 2
Sai ki daura mai a wuta in yayi zafi Sai ki juye dankalin a cikin mai din
- 3
In yayi zakiga yafara Dan ja Sai ki kwashe
- 4
Zaki fasa kwanki saiki yanka mai tumatir da albasa Sai kisa Maggi da Dan gishiri kadan da ruwa Dan kadan
- 5
Sai kisa pan dinki a wuta kisa mangyada dan kadan in yayi zafi saiki juye kwan in yasoyu Sai ki nadeshi ki yayyanka
- 6
Sai ki juye dankali da kwanki a plate shikenan.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8858766



sharhai