Crispy yam nuggets

Inason sarrafa doya sosae nakanyi duk abinda nagani anyi da (irish potatoes)da ita tnayin dadi sosae.kuma da wannan lokaci mae albarka na ramadan an samu chanji dagayin yamballs da doya da kwae kullum💃💃 #1post1hope
Crispy yam nuggets
Inason sarrafa doya sosae nakanyi duk abinda nagani anyi da (irish potatoes)da ita tnayin dadi sosae.kuma da wannan lokaci mae albarka na ramadan an samu chanji dagayin yamballs da doya da kwae kullum💃💃 #1post1hope
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki feraye doyarki ki yanka ki wanke,kisa salt da sugar da ruwa ki dafa har sae tayi lugufff...
- 2
Ki jajjagah,albasa,attaruhu,ginger,garlic,Maggi,curry da thyme.sannan ki zuba daffafiyar doyarki ki daka sosae komae y hade,ki zuba flour dinki a bowl karami kisa paprika,black pepper da sinadarin dandano guda 1 ki juya kisa a side...
- 3
Bayan kin daka doyar saeki kwashe a wani kwanon,nan ga golden morn dinmu,kwae da spicy flour dinmu...
- 4
Ki dan shafa oil kadan a hannunki,ki dibi hadin doyar madaedaeci ki mulmula da dan tsaho,bayan kin mulmula saeki dinga danna saman da kasan a plate sannan ki sake mulmula yadda zae baki shape mae kyau....
- 5
Bayan kin gama mulmulawa duka...
- 6
Saeki saka acikin spicy flour dinki ki juya ko ina y samu,sannan kisa a ruwan kwae,daga karshe kisa a garin golden morn/breadcrumbs/crushed cornflakes
- 7
Hka zakiyiwa kowanne harki gama duka.saeki soya a hot oil...
- 8
Ki soya duka both sides din har yayi golden brown,sannan ki kwashe kisa a colander ko tissue don rage man jikin.
- 9
Alhamdulillah mungama saura ci... 💃💃😋
- 10
Yna da dadi sosae da kunu😋😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
























sharhai (6)