Burodin fulawa Mai zagaye

Salwise's Kitchen @cook_16516066
Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan hadin mu kamar haka
- 2
Da farko za'a jika yeast,sikari da ruwan dumi.. Har sai ya kumburo
- 3
Sai a zuba bota, mangyada da madara.Sannan a dauko yis da sikariñ da aka jika a zuba,a jujjuya har su hade,sai a zuba fulebo a kuma jujjuyuwa,idan yayi karfi dayawa a dan kara ruwan dumi.A rufe a ajiye a wuri mai dumi na minti talatin,domin ya tashi
- 4
Gashi yadda yàyi.Sai a murza sosai,anayi ana zuba fulawa,bayan ya tashi kenan,Saññan ayi mulmula,à shafa bota barbada fulawa a àbin gasawa a jera
- 5
Sai a narka bota a shafa a saman
- 6
A zuba yashi a tukunya,a dora burodin a rufe,a barshi ya gàsu
- 7
A zuba wuta a saman murfin,saboda saman ya gasu
- 8
Gashi bayan ya gasu.,har cikin burodin.Aci lafiya.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10041465

















sharhai