Whipped cream pudding

Bashi da wahala,kuma ba kashe kudi da yawa uwa uba ga dadi 😋
Whipped cream pudding
Bashi da wahala,kuma ba kashe kudi da yawa uwa uba ga dadi 😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki samu madara ki raba ta biyu,ki kawo tukunya ki zuba rabin madarar a ciki ki zuba ruwa kofi uku da siga ki juya sosai.
- 2
Abu na biyu se ki dakko wata roba da ban ki zuba daya rabin madarar a ciki,whipped cream,cornflour se ruwa kofi biyu ki juya su sosai.
- 3
Abu na uku se ki dora tukunyar da kika dama madara da suga ki dora a kan wuta ki rage wutar kar tai yawa kuma kar tai kadan,se ki ta juyawa d wisker ko chokali saboda gudan kamawa.kita juyawa har se madarar ta tafasa.
- 4
Abu na huda se ki kawo kwabin whipped cream da kikayi ki zuba a ciki se ki fasa kwai shima ki zuba a ciki se ki dan sake rage wuta kadan se ki ta juyawa zakiga yana yin kauri da ya fara kauri se barshi iya yadda kikeso se ki kashe wuta ki sauke shi.
- 5
Abu na biyar bayan kin saukeshi se ki rabashi biyu rabi ki barshi fari haka rabi kuma kisa cocopowder ki juya sosai ze koma chakuleti.
- 6
Se ki zuba a kofi zaki iya sha da zafin shi haka za kuma ki iya bari ya huce kisa a fridge ye sanyi sosai.😋😋😋
Similar Recipes
More Recipes






sharhai