Umarnin dafa abinci
- 1
Ki yanka kabewarki kananu ki ajiyeta a gefe da albasa da tumatur ki'ajiye gefe ki jajjaga attaruhu da tafarnuwa da koren tattasai
- 2
Ki dora mai awuta yadanyi zafi ki zuba kabewa aciki kiyi ta juyawa ki zuba yakuwa ciki da kazarki kiyi ta juyawa ki rufe
- 3
Zuwa minti 5 sai kikuma juyawa ki kawo albasa da tumatur da attaruhu ki juya ki rufe.
- 4
Kiyi ta juyawa don kar ya kama inya nuna sai ki rinka murje kabewan kina kara ruwa kadan kikawo spices kizuba da masu dandano ki rufe
- 5
Zuwa 10 ki zuba curry shikenan kingam a sai aci da shinkafa ko taliya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11029211




sharhai