Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fere doya ki wanketa ki yankata sannan ki tafasa
- 2
Saiki wanke tarugunki da albasa (ya danganta da yadda kikeson yaji)saiki jajjagasu,
- 3
Bayan doyarki ta dahu saiki zubeta cikin kwando ki barta ta huce,sannan ki dan dakata a turmi amma kada tayi laushi saiki hadeta da Tarugu da albasarda kika jajjaga,sannan kisa maggi da gishiri ki juyasu da kyau saikin tabbatar komai ya hade
- 4
Saiki fara dunkula su kamar kwallo kina ajewa gefe harki qare
- 5
Ki tabbatar baki matseshi kwarai ba Kuma baiyi saka-sakaba
- 6
Saiki fasa kwai kisamishi gishiri kadan ki kada shi
- 7
Saiki aza kwanon suya ki zuba Mai,idan yayi zafi saiki riqa tsoma kwallon da kikayi cikin kwai kina soyawa har ki qare,Zaki barshi yayi brawn kadan sannan ki kwashe
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11068342




sharhai