Shawarma

#Shawarma wannan hadin nakanyima maigidana shi sosai saboda yanajin dadinsa yakanso ko yaushe yakasance da wannan hadin shawarma
Shawarma
#Shawarma wannan hadin nakanyima maigidana shi sosai saboda yanajin dadinsa yakanso ko yaushe yakasance da wannan hadin shawarma
Umarnin dafa abinci
- 1
BIREDIN SHAWARMA:- zaki samu roba ki zuba kayan hadinki gaba daya kisa ruwa anma kar ki ida zube kofin ruwan kadan kar kwabinki yayi ruwa
- 2
Ga kwabinki sai ki ajiye yayi minti goma,bayan minti goma sai ki sake danna kwabin sai ki rabashi gida bakwai sai ki dauki daya
- 3
Ki mulmula yayi fadi sai kisa ga kasko Wanda bai kamawa sai ki barshi idan dayan gefen yayi sai ki juya gefen shima yayi,sai kisamu waje ki rufe ko tawul haka saboda kar ya bushe
- 4
HADIN NAMA:-zaki samu namanki ki yanka shi da tsawo
- 5
Sai ki zuba namanki a roba wadda takeda murfi,sai kizuba sauran kayan hadinki dakken tafarnuwa,citta,tarugu,magi,kori,kayan kamshi dakuma mangida,sai ki rufe robe ki ajiye cikin fridge ko freezer har awa guda
- 6
Bayan awa guda sai ki aza kaskonki kisa mangida,albasa,sai kisa hadin namanki kina juyawa har ruwan naman ya game jikinsa sai ki kwashe ki ajiye gefe
- 7
HADIN BAMA:-Zaki samu mazubi mai kyau sai ki zuba kayan hadinki ki yamutsa ya game sai ki ajiye gefe
- 8
HADIN SHAWARMA:-ga kayan hadin shawarma dinki
- 9
Sai ki dauko biredin shawarma ki shafa masa hadin bama,sai ki zuba yankakken kabeji
- 10
Sai ki jera namanki,dakuma cucumba
- 11
Sai ki jera soyayyen dankalinki dakuma karas dakika goga
- 12
Sai kisake saka kabeji dakuma hadin bama,sai ki nade shawarma dinki
- 13
Sai ki shafa mai ga kasko Wanda bai kamawa ki aza shawarma dinki saboda komai ya game ajikinsa,ko kisa cikin abun dumama abinci(microwave)
- 14
Ga shawarma nan sai aci lafiya
Similar Recipes
More Recipes































sharhai