Shawarma

Delu's Kitchen
Delu's Kitchen @delu2721
Sokoto State

#Shawarma wannan hadin nakanyima maigidana shi sosai saboda yanajin dadinsa yakanso ko yaushe yakasance da wannan hadin shawarma

Shawarma

Masu dafa abinci 14 suna shirin yin wannan

#Shawarma wannan hadin nakanyima maigidana shi sosai saboda yanajin dadinsa yakanso ko yaushe yakasance da wannan hadin shawarma

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. biredin shawarma
  2. Fulawa 2,1/2 cups
  3. 1/2 tspYeast
  4. Farar hoda(baking powder)1tsp
  5. 1 cupRuwa
  6. 1 tbspSuga
  7. 1 tspGishiri
  8. 2 tbspMangida
  9. HADIN NAMA (MARINATING)
  10. Nama Rabin kilo
  11. Danyar citta Rabin babba
  12. Tafarnuwaguda 3
  13. Maangida 1 tsbp
  14. 2Maggi
  15. Tarugu da albasa
  16. 1 tspKori
  17. 1 tspHadin kayan kamshi
  18. hadin bama
  19. 5 tbspBama
  20. 3 tbspKetchup
  21. 1 tbspMnadara
  22. 1/2 tbspSugar
  23. 1 tbspRuwa
  24. hadin shawarma
  25. Biredin shawarma
  26. Hadin nama
  27. Hadin bama
  28. Kabeji
  29. Karas
  30. Cucumba
  31. Soyayyen dankalin turawa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    BIREDIN SHAWARMA:- zaki samu roba ki zuba kayan hadinki gaba daya kisa ruwa anma kar ki ida zube kofin ruwan kadan kar kwabinki yayi ruwa

  2. 2

    Ga kwabinki sai ki ajiye yayi minti goma,bayan minti goma sai ki sake danna kwabin sai ki rabashi gida bakwai sai ki dauki daya

  3. 3

    Ki mulmula yayi fadi sai kisa ga kasko Wanda bai kamawa sai ki barshi idan dayan gefen yayi sai ki juya gefen shima yayi,sai kisamu waje ki rufe ko tawul haka saboda kar ya bushe

  4. 4

    HADIN NAMA:-zaki samu namanki ki yanka shi da tsawo

  5. 5

    Sai ki zuba namanki a roba wadda takeda murfi,sai kizuba sauran kayan hadinki dakken tafarnuwa,citta,tarugu,magi,kori,kayan kamshi dakuma mangida,sai ki rufe robe ki ajiye cikin fridge ko freezer har awa guda

  6. 6

    Bayan awa guda sai ki aza kaskonki kisa mangida,albasa,sai kisa hadin namanki kina juyawa har ruwan naman ya game jikinsa sai ki kwashe ki ajiye gefe

  7. 7

    HADIN BAMA:-Zaki samu mazubi mai kyau sai ki zuba kayan hadinki ki yamutsa ya game sai ki ajiye gefe

  8. 8

    HADIN SHAWARMA:-ga kayan hadin shawarma dinki

  9. 9

    Sai ki dauko biredin shawarma ki shafa masa hadin bama,sai ki zuba yankakken kabeji

  10. 10

    Sai ki jera namanki,dakuma cucumba

  11. 11

    Sai ki jera soyayyen dankalinki dakuma karas dakika goga

  12. 12

    Sai kisake saka kabeji dakuma hadin bama,sai ki nade shawarma dinki

  13. 13

    Sai ki shafa mai ga kasko Wanda bai kamawa ki aza shawarma dinki saboda komai ya game ajikinsa,ko kisa cikin abun dumama abinci(microwave)

  14. 14

    Ga shawarma nan sai aci lafiya

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Delu's Kitchen
rannar
Sokoto State
My name is Aisha Delu Aliyu known as Delu's Kitchen ,I love cooking ,cooking is my fav....
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes