Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko Zaki tankade fulawa ki zuba Mai da gishiri ki kwaba kamar kwabin meatpie sai ki rufe kamar minti 20
- 2
Kisa mai a pan sai kisa tafarnuwa da nikakken nama kisa albasa da dandano da kayan kamshi ki juya ki rufe shi har ruwansa ya tsotse
- 3
Ki dauko kwabin ki gutsura kanana ji shafa mai ajikin ko wanne ki fadada shi suyi kai daya sai ki hada kamar guda biyar kiyi rolling ki Dora non_stick pan a wuta amma karki cika wuta sai ki gasa ki juya dayan barin shima ki gasa
- 4
Sai ki fitar da round shape ki raba shi gida hudu kamar triangle.ki cire a hankali. ki kwaba wata fulawarkikina zuba kayan hadinki kina likewa har ki gama
- 5
Sai ki soya a Mai
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11899484





sharhai