Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki jika waken ki mai kyu da kika gyara, kibashi 3 minutes,sai ki sa a turmi ki jajjaga, idan kinga bawon ya fita sai kisa ruwa ki wonke ki cire bawon gaba daya sai yazama ba bawo acikinsa,sai ki zuba a roba,ki saka attarugu da albasa ki kai a nika miki yayi laushi, in an kawo daga nika, sai ki xuba manja, maggi, curry,gishiri sai ki xuba dafaffen kwai ko fish naki inkinaso,sai ki karawa kullin ruwa,yenda komai zaiyi daidai, sai ki kawo leather alale,ki bude ki dinga sawa yenda kikeso
- 2
Inkin gama kullashi size da kikeso,sai ki daura ruwa a wuta kibarshi ya tafasa, sai ki kawo kulin alalen ki ki dinga sawa daya bayan daya,kixuba dukka sai ki dauko bakar leather ki rufe saman tukunyan kafin ki rufe da murfi, sai ki rage wuta daidai kibarshi, inya nuna zakiji yana kanshi, kawai sai ki soya manja naki kici alalenki da manja da yaji....
Similar Recipes
More Recipes




sharhai