Fried rice

A gsky ina son shinkafa sosai shyasa nake sarrafawa ta hanyoyi daban daban kuma alhmdllh iyalai na sunyi farin ciki sosai d cin wannan
Fried rice
A gsky ina son shinkafa sosai shyasa nake sarrafawa ta hanyoyi daban daban kuma alhmdllh iyalai na sunyi farin ciki sosai d cin wannan
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki yanka kayan lambunki kanana
- 2
Ki tafasa ruwa, ki wanke shinkafarki ki zuba, idan shinkafar ta fara alamar dahuwa, da garas-garas din ta sai ki sauke, ki tace
- 3
Ki dora man ki a wuta, idan yayi zafi sai ki zuba kayan lambunki dama kin yanka albasa slice, da attarugu kanana duka sai ki zuba, ki yi ta juyawa, idan suka fara laushi sai ki zuba shinkafarki
- 4
Da maggi da gishiri da curry, ki yi ta juyawa har sai shinkafar ta karasa dahuwa duk tare da kayan lambun, idan tayi za ki ga ta yi wara-wara ta yi kyau a fuska, kayan lambun kuma zai fito a ciki ya yi shar-shar.
- 5
Saiki wanke kifinki ki gyara shi ki soya saiki saka a cikin fried rice din shknn kin kammala fried rice Kuyi girki cikin farin ciki d annashuwa 😍😘
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





sharhai (4)