Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko dai ga kuli kuli mai kayan hadi a ciki, sai ruwa da albasa na yanka. Sai na tafasa nama namai hadin su Maggi da kayan kamshi ya dahu luguf har ya tsotse ruwan, sai nai ta juya naman har ya Fara kamawa kadan. Sai na juye shi.
- 2
Sai na dora mai a wuta da yayi zafi sai na juye naman naita juyawa.
- 3
Bayan minti biyu na zuba hadin kuli kulin naita juyawa.
- 4
Sai na zuba albasa na yayyafa ruwa kadan na rufe tukunyar.
- 5
Bayan rabin minti na bude na Kara xuba kuli kulin na juya sosai
- 6
Na tabbatar ko ina yaji hadin sai na Kara barbada albasa na juye a faranti.
- 7
Aci dadi Lafiya😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12879226

























sharhai