Chin chin

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Kawatace tazomin mai musamman tundaga jos shine namata wannan cincin din don tatafi da ita kuma taji dadinshi sosai har tana cewa dama zansakeyin wani na aykamata har zuwa jos

Chin chin

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Kawatace tazomin mai musamman tundaga jos shine namata wannan cincin din don tatafi da ita kuma taji dadinshi sosai har tana cewa dama zansakeyin wani na aykamata har zuwa jos

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa kofi bakwai
  2. Kwai hudu
  3. Butter leda daya
  4. Baking powder chokali babba daya
  5. Madarar ruwa gongoni daya
  6. Nutmeg rabin chokalin shayi
  7. Sugar kofi daya da rabi
  8. Sai ruwa don kwabawa
  9. Gishiri rabin chokalin shayi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zakitankade fulawa kizuba a babban roba sai kisa sugar da baking powder tareda nutmeg da gishiri ki jujjuya sosai komai yahade sai kuzuba butter ki mursika sosai yanda butter zaishiga jikin

  2. 2

    Sannan kixuba kwai da madarar ruwa ki jujjuya sai kisa ruwa kadan kadan kina kwabawa har yayi dai dai. Amma karkisa ruwa dayawa sbd kar yamishi yawa

  3. 3

    Bayan kinsa ruwa sai ki kwaba sosai yayi laushi sannan kirufe ki ajiye agefe zuwa minti goma ko shabiyar

  4. 4

    Bayannan sai kidauko kisake kwabawa sannan kirabata gida uku sai kidauko dayan kimurzata tayi fadi sosai sannan kidauko wuka kiyanyanka ta yanda kikeson girmanta sannan kidaura mai a wuta idan yayi zafi sai kidan rage wutan sannan kirika zubawa kina soyawa

  5. 5

    Haka zakiyi tayi har kigama. Shikenan aci dadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes