Soyayyen kifi

Munason kifi sosai nida oga shiyasa nakeyi mana dabarun sarrafa shi kuma munji dadin suyar kifinnan.
Soyayyen kifi
Munason kifi sosai nida oga shiyasa nakeyi mana dabarun sarrafa shi kuma munji dadin suyar kifinnan.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na wanke kifin tatas da lemon tsami na kankare na cire dattin cikin kifin na saka shi a kwando ya tsane.
- 2
Sannan na wanke attaruhu da albasa na jajjaga na daka tafarnuwa saina zuba mai a kwano na juye attaruhu da albasa da tomeric da tafarnuwa da kayan kamshin na zuba maggi saina jujjuya na ajiye a gefe saina dauko kifin nan na zuba gishiri na jujjuya sannan na saka brushes na shashshafa source dinnan a jiki na saka a fridge tsahon 30 minutes.
- 3
Saina zuba mai a kasko da yayi zafi na dinga saka kifin nan a ciki harya soyu na kwashe.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes







sharhai