Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki barza dambun ki kaman yanda ake yin na dambu,sai ki wanke ki sa a wuta ya Fara Yi idan ya kusa nuna sai ki sa wankakken zogale a ciki ki juya su su juyu da kyau sai ki rufe har ya karasa nuna
- 2
Sanna sai mu koma ga miyan cabbage din.zaki yanka cabbage dinki dice,Haka ma carrots dinki,sanna shima Irish dinki ki yanka dice,sai albasa ki ya da shi yauj dogo dogo.
- 3
Da farko Zaki sa Mai a wuta ki soya kayan miyan ki,kisa Mai dukan kayan Dan Dani da ake bukata.
Daga Nan Kuma dama kin San dafa Irish potatoes dinki sai ki zuba ki zuba albasa ki zuba carrots su Dan Yi kaman minti 5 suna soyuwa sai ki kawo cabbage din ki zuba
- 4
Bayan kin sa cabbage sai ki zuya shi don su hade sai ki Dan zuba ruwa kana Kofi 2 sai ki rufe har sai ya nuna daga Nan sai ci🤤
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





sharhai