Faten tsakin masara

teezah's kitchen @cook_14114675
Ina hausawan suke ne, gafa gargajiya tazo, wato fate
Faten tsakin masara
Ina hausawan suke ne, gafa gargajiya tazo, wato fate
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki soya manja da man gyada tare da albasa da daddawa da citta, sai kuma a zuba jajjage a soya
- 2
Zaki zuba ruwa isasha, ki zuba Maggie da gishiri ki rufe ruwan ya tafasa
- 3
Zaki wanke tsakin ki rege, kananan barji yafi kyau da fate, sai ki zuba ki jujjuya a ruwan
- 4
Zaki rufe ki dinga dubawa idan yayi kauri ki kara ruwan zafi, idan ya kusa dahuwa
- 5
Sai ki zuba alayyahun da kika yanka kika wanke, manyan yanka yafi dadi
- 6
Sai ki rufe ya sulala sai ki kashe wutar.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16320676



sharhai (2)