Kosan Rogo

Hmmm... Nasiya dafaffen rogo domin inci, senaji inason cin koson rogo abinka da kwadayin masu ciki😋😂 shine na maidata koson rogo.. Yarana da megidana sunason kosan rogo sosaiii....
Kosan Rogo
Hmmm... Nasiya dafaffen rogo domin inci, senaji inason cin koson rogo abinka da kwadayin masu ciki😋😂 shine na maidata koson rogo.. Yarana da megidana sunason kosan rogo sosaiii....
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaki bude rogonki ki cire wannan kashin na tsakiya kisa a kwano. Seki hada kayayyakin dazaki amfani dasu guri daya
- 2
Bayannan zaki murje rogon da hannunki ko marsher dinki harse yazama gari gari, seki zuba dakakken kayan miyanki da yankakken albasarki
- 3
Bayannan seki zuba magginki, bansa gishiriba sbd bancika amfani da itaba
- 4
Bayannan seki sa hannunki ki cakuda harse sun hade jikinsu. Toh ananne zakisa karin kwaki har inkinga kwabinki yana kama hannunki gudun karya watse a mai seki zuba garin kwaki ki daureshi.
- 5
Bayannan seki fara mulmulashi kwallo.
- 6
Bayannan seki Dan rinka mammatsasa ya bude, seki jera a faranti
- 7
Sekisa man gyadarki a kaskon suya. Ki soyashi harse yyi golden brown.
- 8
Asa a faranti akuma sa yaji. Aci dadi lpy
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
















sharhai (11)