Farfesun kifi (cat fish pepper soup)

teezah's kitchen @cook_14114675
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki wanke kifi da ruwan zafi da gishiri, idan yaukin ya fita sai ki sake wanke shi a ruwan da kika saka vinegar murfi daya, za kifa kifin ba yauki kuma ba karni
- 2
Zaki dora a wuta kisa ruwa Dan dai dai sabida baya son ruwa, yana saurin dahuwa kada ya fashe
- 3
Zaki zuba mixed spice dinki da Maggie sai ki rufe
- 4
Idan ya taso sai ki zuba jajjagen ki da albasar da kika yanka ki rufe ki sa wutar yar dai dai kar ki cika
- 5
Zaki bashi kamar 10-15 minutes sai ki sauke, a ci dadi lafiya
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16474267









sharhai (2)