Wainar shinkafa

Ummu Aayan @Sadiyanahajakitchen
Ina San Masa da kuli kuma kowace irin Masa ce ta shinkafa,semo ko ta gero
Wainar shinkafa
Ina San Masa da kuli kuma kowace irin Masa ce ta shinkafa,semo ko ta gero
Umarnin dafa abinci
- 1
Ma kwaba garin shinkafar da ruwa ajiye yayi 3hrs
- 2
Se na tafasa ruwa kadan sannan na Debi kullun shinkafar 2tsp na zuba nayi ta juyawa har ya dahu sannan na barsh ya huce su na Kara Dan ruwa na dama sanan na juye shi akan wancan garin shinkafar
- 3
Na kawo nono, baking powder,Dan gishiri, sugar da yeast din na zuba na jujjuya se na rufe ya tashi tsawon 25-30min sannan na kawo albasa da na bare na wanke Mai mata yankan sirisiri na zuba a ciki
- 4
Na Dora tanda a wuta na zuba Mai na soya
- 5
Zaki iya ci da miya,sugar ko kulikuli.
Na fi so da kulikuli so enjoy 😋😋🤤
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16736717






sharhai (4)