Miyar Rama da gyada

Wannan miyar gargajiya ce wacca nake jin dadinta sbd dandanon tsami tsaminta #miya
Miyar Rama da gyada
Wannan miyar gargajiya ce wacca nake jin dadinta sbd dandanon tsami tsaminta #miya
Umarnin dafa abinci
- 1
Da Farko zaki Wanke ramarki da kyau ki yayyanka ta ki sake wankewa se ki tsane ki ajiye ah gefe.
- 2
Ki dauko namanki ki wanke ki saka masa kayan qamshi da na dandano,se ki tafasa ki soya sama sama ki ajiye ah gefe.
- 3
Se ki samu Kayan miyanki ki jajjaga da Albasa Kadan,ah gefe kuma zaki sake yanka Albasa da yawa ki ajiye ah gefe.
- 4
Ki dauko jajjagen kayan miyanki ki saka mai kadan ki soya sama sama,se ki tsayar da ruwa ba me yawa ba,se ki zuba namanki da kayan dandanon ki,ki rufe ya bararraka naman ya samu yayi laushi lugub,se ki dauko ganyen ki zuba ah kai se ki dan dinga ruwan kanwa ko tokan miya ya dan kashe miki tsamin.se ki rufe ki bari ganyen ya nuna.
- 5
Bayan ya nuna se ki dauko albasarda kika yanka ki zuba akai ki rufe ya dan qara nuna se ki dan dama markadadden gyada da ruwa kadan se ki zuba kan miyan.
- 6
Yana hade jikinsa shikenan miya tayi se ah mata tuwo me laushi.
Similar Recipes
More Recipes












sharhai