Egusi soup

#miya Shi miyan egusi dai yana da hanyoyin da akeyi ta da dama a yau dai na zo muku da yadda akeyin wani miyan ku biyoni kuji yadda nayi wannan miyan
Egusi soup
#miya Shi miyan egusi dai yana da hanyoyin da akeyi ta da dama a yau dai na zo muku da yadda akeyin wani miyan ku biyoni kuji yadda nayi wannan miyan
Umarnin dafa abinci
- 1
Kina bukatan ki shirya duk wani Kayan da zaki bukaci Damon yin miyan nan
- 2
Zaki had a Duk protein dinki ki dafa Amma nan saka pomo da kifi ba dan suna da laushi. Zaki daura naman a wuta idan ta ragu sai ki zuba su pomon da kifin. Cikin naman na tafasa da ginger Ina matukar son ginger a girki gaskiya
- 3
Sai ki zuba manja da enough ruwa da zai dafa miki miyan
- 4
Ga kalolin magin da nayi anfani dasu nan. Sai ki rufe har ya tapaso
- 5
Sai ki zuba crayfish dinki kam ki rufe
- 6
Idan ruwan ya tafasa Daman kin dama garin agushin cikin wani kwano daban sai kina jefawa ciki da cokali kamar jefan kosai Amma da karamar cokali zakiyi wannan kar tayi girma sosai
- 7
Sai ki rufe karki gauraya bayan dan wassu lokuta sai ki bude ki juya
- 8
Daga nan sai ki zuba jajjagen attarugu, shombo da black pepper irin wannan local da ake saidawa a kasuwa yafi kamshi a miya
- 9
Sai ki kawo irunki daddawan yarbawa ki zuba aciki
- 10
Sai ki zuba ganyen ughu aciki
- 11
Sai ki gauraya dakya
- 12
Ga shi nan yadda zai kasance
- 13
Note wannan miyan zaku iya anfani da bitter leave ko alayyahu maimakon ughu, zaki iya anfani da duk naman da ya miki cikin miyan nan, zaki iya soya manja da kayan miya ba lallai sai kin sa direct ba Amma ki gwada yin hakan zakiji chanjin taste kuma saka daddawan ba dole ba. Idan kunaso zaku iya anfani da mai ko ayi mixing da manja
- 14
Ga miyan ta kammala
- 15
Naci nawa da tuwon sakwara
Similar Recipes
More Recipes




















sharhai (22)