Kwadon Rama

Chef Uwani. @cook_14144607
#kanostate Veggies are good for your health. Love them. Eat them.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki dora ruwa a tukunya ki dafa. In ya kusa dahuwa sai ki zuba ramarki a ciki daidai buqata.
- 2
In ya tafaso. Ya dahu na minti 2 sai ki kashe gas ki barshi a cikin ruwan na minti 3.
- 3
Ki daka Kulikuli da Maggi da gishiri. Ki hada Tafarnuwa da Citta da curry. Ki daka sosai.
- 4
Ki yanka albasa da green pepper da tumatir
- 5
Ki tsane ramar Ki wanke ta a ruwa. Idan kina san dan tsami-tsami kar ki wanke ta sosai. Sai ki tsane ta. Ki zuba Kulikuli a cikin su albasa ki zuba ruwa kadan ki cakuda. Sai ki zuba ramarki a ciki Ki juya. In komai yaji Shknan. In beji b ki kara
- 6
Idan kina so ki barbada Jan yaji. Aci lafia 💞
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/6594119








sharhai