Umarnin dafa abinci
- 1
A zuba ruwa a tukunya dora a wuta a rufe abarshi ya tafasa sai a tankade garin dawar kadan a dama da ruwa sai a rage tafasasshen ruwan a ruwa damamman dawar cikin tukunya a gauraya da muciya sosai
- 2
Sai a rufe a barshi ya dahu sosai sai anga idan an daga shi da muciya yana yauki Sai a rage talgen kadan a cup sannan atuka da sauran garin dawar anayi ana zuba wannan talgen da aka rage har sai ya hade jikinsa
- 3
Sai a barshi ya dahu Amma arage wutar sosai idan yayi sai a tuka a kwashe
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/7270826



sharhai