#Garau-garaucontest

Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zakisa ruwa a tukunya idan ya tafasa sai ki zuba shinkafa,sannan ki daura wake ma daba,amma wasu suna hadasu duk a tukunya daya ne.
- 2
Idan shinkafan ya tafasa kadan sai juye a kwandon tsane shinkafa ki sake sa wani ruwan kadan a tukunya kisa gishiri,shima wake ki sauke ki tsiyaye ruwan saiki hada shinkafa da waken a tukunya daya ki rage ruwa harya nuna ki sauke.
- 3
Ki wanke kabejin ki da tatas da tumatur da kokunba duk ki yanka su ki ajiye a gefe,wasu suna sa albasa idan suna so.
- 4
Ki sake dafa wanki akan wuta ya nuna ki sauke,idan kina da kifi to saiki wanke ki soya a mangyada,idan kuma baki dashi saiki aika soyayye shikenan ki dama kin soya mangyadan ki da albasa.
- 5
Ki zuba abincin a faranti kisa mangyada akai sannan ki zuba kayan hadi su kabejin kenan ki fasa maggi akai kina diban yaji kina ci😍 musamman idan kika sa kifi dad'in ta ba'a magana...
Similar Recipes
More Recipes



sharhai