Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki duba wakenki ki cire dattinda gareshi, sai ki wanke tass kira a tukunya ki zuba ruwa a kalla kofi uku babba ki dora bisa wuta
- 2
Idan waken yayi kasa alamar ya dauko nuna kenan sai ki zuba shinkafa
- 3
Akalla ta samu minti sha biyar sai ki wanke
- 4
Ki kara sauki ruwa a tukunya ki zuba farin margin ki da gishiri kadan ki zuba shinkafa da waken ki juya sosai sai ki maida kan wuta
- 5
Ki samma yaji da citta da maggi ki daka sai sun daku sannan ki balla tafarnuwa kadan kisa ki kara dakawa sai sun daku
- 6
Ki soya man gyada da albasa
- 7
Ki yayyanka kayan lambun ki ki sa a mazubi mai kyau
- 8
Ki soya kifinki sai ya soyu ki kwashe
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/7782864




sharhai