Garau garau

Ayau inaso innuna asalin yanda ake garau garau Wanda kakan ninmu keyi kafin,kuma lokacin da shi akeyi kafin azo da abun a zama nance bari in tuno maku baya#garaugaraucontest
Garau garau
Ayau inaso innuna asalin yanda ake garau garau Wanda kakan ninmu keyi kafin,kuma lokacin da shi akeyi kafin azo da abun a zama nance bari in tuno maku baya#garaugaraucontest
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki sa ruwa acikin tukunya ki daura akan wuta,idan ya tausa sai ki wanke shinkafa kiss acikin ruwan ki barshi ya tafasa na minti biyu,idan lokacin yayi sai ki sauke ki samu a in tsama ki juye shinkafan sai kisa acikin roba kisa ruwa kikara zubar da ruwan,kisa shinkafan a tukunya da ruwa kadan sai ki barshi ya kara nuna,idan yayi ki sauke ki ajiye a gefe
- 2
Zaki gyara wake ki tsince duwatsu kisa ruwa acikin tukunya ki daura akan wuta idan ya tausa sai ki wanke waken ki zuna acikin,zaki barshi ya nuna sosai,idan ya nuna sai ki samu abin tsama ki juye aciki sai kira sa ruwa ki daura kisa acikin abin tsama ki ajiye a gefe
- 3
Zaki samu tukunya kisa akan wuta kisa mai da albasa ki soya man idan yayi ki ajiye a gefe yasha isaka, sai ki zuba shinkafa acikin filat kisa wake akai sai kisa gishiri da yaji
- 4
Ya ka mata Ku gwada wannan garau garau din shine na asali
- 5
Ina taya cookpad murnan cika shekara biyu
Similar Recipes
More Recipes




sharhai