Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fasa kwai kisa a kwano kisa Yis da siga kisamu ruwan dumi kisa aciki sai ki kada sosai ki barshi ya yayi minti biyar
- 2
Sai kisamu roba kisa filawa,bakin fauda,madara da bota ki juya sosai sai ki dauko yis da kika jika kisa zuba acikin filawan ki kwaba su hade jikin su kwabin zaiyi kaman na biredi sai ki barshi yayi min arba'in
- 3
Idan yayi ki kara bugawa sosai sai kisa man gyada a hannunki kirinka iban kwabin kina mul mulawa yanda kikeson girman sai ki barshi yayi minti goma
- 4
Idan yayi zaki sa man gyada akan wuta yayi zafi sai ki sa dan yatsanki guda daya a tsakiyan kwabin yayi rami kisa acikin mai amma kar ki cika wuta,idan wuta yayi yawa zai kone haka zakiyi har ki gama soyawa
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/7969360




sharhai