Miyan alayyaho
Ganye nada mahimmanci ajikin dan adam #kadunagoldenapron
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki wanke timatir,tarugu,tattasai da albasa guda daya sai ki nika amma kar yayi laushi kisa acikin tukunya ki sa akan wuta,idan ruwan ya tsotse sai kisa manja ki soya miyan idan yayi kisa ruwa kadan da magi
- 2
Zaki sa alayyaho a roba da gishiri kisa ruwa ki wanke ki zubar da ruwan ki kara sawa sai ki zubar da ruwan ki yanka kanana kisa acikin miyan
- 3
Zaki wanke nama ki sa magi guda daya kisa ruwa yanda zai dahu idan yayi kisa acikin miya ki yanka albasa kisa sai ki barshi yayi Monti uku ki sauke za a iya ci da tuwan shinkafa ko shinkafa amma naci nawa da shinkafa
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8203977





sharhai