Shinkafa da source da soyayyan naman kaza da wainar dnkl da zobo

Gaskiya yana da dadi sosai kuma yn birge iyalina
Shinkafa da source da soyayyan naman kaza da wainar dnkl da zobo
Gaskiya yana da dadi sosai kuma yn birge iyalina
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki hura wuta ki dora ruwa a tukunya yatafasa saiki zuba shinkafarki ki rufe idan tayi laushi saiki taceta a matsani sannn saiki maidata tukunya ki rage wuta sai ruwan jikinta y tsotse saiki sauce.
- 2
Sannn shikuma naman kazarki kin wankeshi kin xuba a tukunya kinyanka albasa akai da yar citta da Magi guda biyu saiki dora shi awuta yayi laushi saiki dan barbada gishiri Kadan saiki bari ruwan ydn kama jikin kazar saiki debeta ki dora Mai a wuta yayi zafi saiki soya kazarki tasuyu saiki tsameta a martini.
- 3
Shi kuma dan kalinki kin fereshi saiki tafasa yy laushi ki samu kwano ki zuba ki farfasashi daiki zuba kwanki a kai da yar albasa da Dan Magi ster guda 1 dan karyayi gishi ri saiki soyashi kamar wainar filawa.
- 4
Sai source dinki zaki wanke taruhunku da tattasai da albasarki ita wann miya bata bukatar tomato saidai ishashshiyar albasa zaki sa saiki yi gratin dinsu ki juye a tukunyarki kidan sa ruwa kadan y tafasa saboda gafin tattasai y fita saiki zuba manki kamar ludayi biyu saiki sa kayan Dan danon dai dai yadda kike so da kori idan t soyu saiki juyeta a Abu mai kwau shikenn kin kammala sai ci.
- 5
Zaki dafa subonki saiki tace ki zuba sugar da filebo ki yayyanka coconbar ki kizuba saikisa a firji yayi sanyi ko kuma ki farfasa kankara a coke.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai