Simple Pizza

Na tashi da shaawan cin pizza,sai na qirqiri wannan #1post1hope
Simple Pizza
Na tashi da shaawan cin pizza,sai na qirqiri wannan #1post1hope
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki saka manki da nikakkan namanki akan pan
- 2
Saiki ta juyawa idan ya juyu sai ki zuba albasanki da attaruhu Wanda kka jajjagasu
- 3
Sai ki zuba kayan dandanonki
- 4
Ki ta juyawa har sai ya yi, zakiga alamun ya soyu
- 5
Ki tankade fulawarki a roba ki zuba yeast da gishiri ki kwaba kada kwabin yay ruwa sosai
- 6
Sai ki barshi ya tashi na tsahon minti goma ko Sha biyar
- 7
Sai ki dauko tray naki na oven naki, sai ki shafa mai ko butter ki barbada fulawa a kai
- 8
Sai ki dauko wannan kwabin naki ki dinga fadashi a jikin pan dinnan
- 9
Amma ana son tsakiya yay ciki, gefe gefen Kuma yay sama
- 10
Saikiy gasa kasan idan ya gama sai ki koma saman ma,
- 11
Sai ki dauko hadin naman naki ki zuba a jikin ko ina ya samu, sannan ki Dan zuzuba mayonnaise naki a Kai,
- 12
Sai ki mayar cikin oven din yay kamar mintina 3
- 13
Zakiga mayonnaise dinki tayi kamar cheese shikkenan ya kammala
Keywords
Similar Recipes
More Recipes








sharhai