Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki gyara waken ki ki jikata ki surfata, ki cire mata dissan ta ki wanke tas ki gyara tattase da albasa ki yanka acikin markaden waken ki ki markada ablender ko ki kai injin markade,
- 2
Ki dauki kullin waken ki kisa gishiri ki kada shi yayi taushi sosai, ki yanka albasa yisi yisi aciki
- 3
Ki dauki kasko ki daura wuta ki zuba mai in yayi zafi ki hau suya, in ya soyu kaman haka sai ki kwashe, kisha da kunu ko ruwan lipton iya dadi.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/9068259





sharhai