Miyar busassar kubewa da man shanu#3006
Tana da dadi sosai
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki tafasa naman ki,ki niqa tattasai,albasa da tarugu ki ajiye gefe
- 2
Sai ki zuba manja a tukunya,kisa albasa ki soya shi,sai ki zuba jajjagen ki (kayan miya),idan ya soyu sai ki zuba ruwa dai dai yawan da kike bukata,ki zuba namanki da kika tafasa
- 3
Sai ki zuba kayan yajin ki,(daddawa,citta da tafarnuwa)
- 4
Ki saka maggi,gishiri da kayan kamshi,sai ki rufe tukunyar kibar miyar ta dahu sosai,idan kikaga ruwan sun kai yadda kike bukata sai ki dauko garin kubewarki ki zuba a hankali kina juyawa da maburki har tayi kaurin da kike buqata
- 5
Sai ki sauke miyar daga kan wuta don kada ta tsinke
- 6
Sai ki zuba man shanu a kai
- 7
Zaki iyaci da kalar tuwon da kike bukata
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/9379846




sharhai (3)