Dan waken alabo da fulawa

#Dan-wakecontest,ana iya sarrafa dan wake ta hanyoyi da dama,kuma yayi dadi da dandano,shiyasa nima na sarrafa na alabo da fulawa,hakika yayi dadi da kuma tauri gami da sul6i.
Dan waken alabo da fulawa
#Dan-wakecontest,ana iya sarrafa dan wake ta hanyoyi da dama,kuma yayi dadi da dandano,shiyasa nima na sarrafa na alabo da fulawa,hakika yayi dadi da kuma tauri gami da sul6i.
Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan hadin mu kamar haka,garin alabo, fulawa,ruwan kanwa,ruwan kwabawa da kayan lambu da kwai
- 2
Da farko za'a hada alabon da fulawa,sannan a zuba ruwan kanwa ko ungurnu
- 3
Sannan a zuba ruwan a jujjuya
- 4
Idan suka hade kaurin yayi kamar haka
- 5
Sai a Dora ruwa a wuta,idan ya tafasa sai arika gutsira ana sakawa,sai a rufe ba duka ba,saboda kada ya cika ya zuba
- 6
Sai a duba idan ya nuna,ko a dauki guda daya a sanya cikin ruwan sanyi a matsa,idan anji tauri ya nuna,idan ba'aji tauri ba,da saura
- 7
Bayan ya nuna sai a kwashe,a zuba cikin ruwan sanyi mai kyau,a daure saboda danko
- 8
Sannan a zuba a mazubi mai kyau
- 9
Sai a yayyanka,kabeji,tumatur, albasa,cucumber, Karas da dafaffen kwai,a sanya agefe.Sannan a zuba soyayyen mangyada ko manja,da mai da yaji.Aci lafiya.
Similar Recipes
More Recipes













sharhai