Jollof din shinkafa da wake
Dadi ba magana😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaki wanke tukunyanki kiyan ka albasa kisa mai ya soyu
- 2
Seki kawo spices dinki da bushesshen tattashi kizuba su soyu tare inya soyu
- 3
Seki kawo nama kisa ki jujjuya karya kama seki zuba ruwa daidai wanda zai nunar miki shinkafan ki
- 4
Ki kunna wani wuta ki zuba ruwa a tukunya ki daura kitsince waken ki seki wanke kizuba a ruwan ki jefa kanwa su tafasa tare
- 5
Seki koma daya tukunyar ki inya tafasa kiwan shinkafan ki seki zuba kijujjuya kibarshi
- 6
Idan waken ki yadan nuna ba duka ba garas garas haka seki tsaneshi a colander kizuba mishi ruwan sanyi
- 7
In ya nuna ba se kinkara ruwa in be nuna ba ki dan kars kadan shikenan. Aci dadi lfy😋
- 8
Idan shinkafanki ma yakusa nuna seki kawo waken ki dakik wanke kizuba akai ki jujjuya ki barsu su tsotse sauran ruwa
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





sharhai