Kosai (kosan wake)

Ina sha'awar cin kosai musamman saboda yana dauke da sinadarin protein da ke gina jiki. # I post I hope
Kosai (kosan wake)
Ina sha'awar cin kosai musamman saboda yana dauke da sinadarin protein da ke gina jiki. # I post I hope
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki gyara wake, ki tsince duk wanni dattin da ke ciki se ki surfa sama sama a turmi har sai bayan ya rabu da jikin waken sai ki zuba a roba ki wanke tas har se bayan ya fita duka.
- 2
Ki barshi cikin ruwa tsawon minti ashirin
- 3
Bayan minti ashirin se ki cire waken daga ruwa ki zuba tattasai, taruhu, da albasa da kika riga kika wanke kika gyara se a markada har se kullun yayi laushi.
- 4
Zaki buga kullum har tsawon minti ashirin domin kosan yayi kyau yayi laushi kuma. Bayan nan zaki saka dandano da kuma gishiri kadan daidai yanda kike so. A kula kosai yafi son farin maggi, idan baki aiki da farin maggi ba se kin sa ba, gishiri kawai ya wadatar.
- 5
Sannan se ki zuba mai a kwanon suya ki jefa albasa daya wacce ba' a yanka ba domin kamshi a suyar da zakiyi. Idan mai yayi zafi se ki debo kullun waken kina sakawa a cikin ruwan mai daidai girman da kike so kamar haka
- 6
Idan kin gama sakawa se ki barshi ya soyu idan yayi ki juya dayan gefen kamar haka
- 7
Ki bashi lokaci kadan se ki kwashe a colander kamar haka
Keywords
Similar Recipes
More Recipes










sharhai