Gashassen hakarkarin rago

#namansallah wannan salon girki nada dadi sosai. Farko dana fara yinshi ina gamawa aka chinye a Kitchen. Shi nayi a sallah kuma duk wanda suka chi sunche ya musu dadi
Gashassen hakarkarin rago
#namansallah wannan salon girki nada dadi sosai. Farko dana fara yinshi ina gamawa aka chinye a Kitchen. Shi nayi a sallah kuma duk wanda suka chi sunche ya musu dadi
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki wanke hakarkarin ki saka a kwano. Ki zuba barkono baki da garin chitta
- 2
Ki zuba curry da maggi. Ki zuba attarugu
- 3
Ki zuba dakakken tafarnuwa da ruwan lemun tsami da garin coriander
- 4
Ki zuba mai geda ki motsa shi da kyau. Ki saka a fridge na hour 2 ko ki barshi ya kwana. Domin hadin ya shiga chiki
- 5
Ki shafa butter a kan pan saiki jera hakarkarin a kai. Ki gasa na minti 45
- 6
Bayan yayi ki chire shi a wuta
- 7
A wani tukunya ki zuba soy sauce da tumatur na kwalba da garin coriander. Ki saka wuta kadan
- 8
Ki zuba ruwa a chikin kwanon da kikayi hadi ki juye a tukunya
- 9
Ki saka hakarkarin ki motsa da kyau. Ki barshi ya nuna na minti 3
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

























sharhai