Kilishi

Sumy's delicious
Sumy's delicious @cook_13830250
Gombe State, JikadaFari

#NAMANSALLAH Kilishi dai nama ne da akasari ake yin shi a yankin da Hausawa suke a Arewacin Najeriya, ko Arewacin lardin Kamaru, ko a yankin Jamhoriyar Nijar. Ana yin kilishi ne dai da naman shanu, ko rago, ko akuya, ko na rakumi. Ma'abota kilishi sun bayyana shi da zabebben nama wanda sai asalin mahauci dan gado ke yin shi. Mafi shaharar kilishi dai da naman shanu ake yin shi, saboda haka a sakamakon yawaitar shanu a yankin da Hausawa suke ya kai ga haifar da wasu kwararru a harkar gudanar da yin kilishi sannan masuyin kilishi sunabusarda namansu a rana na tsawon kwana uku mukuma na gida mun samar muku sauki ynda zaki sarrafa kilishinki acikin awa daya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Nama
  2. Yajin soya
  3. Gyada soyayya
  4. Dandano
  5. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zakisamu tsokar namanki sai ki yankashi filan filan kamar hka sai ki barbada mishi gishiri kadan

  2. 2

    Zaki kunna oven dinki yayi zafi sannan sai kisa namanki aciki amma wutar kadan kamar na minti goma haka sai zakiga ya fara bushewa kamar haka

  3. 3

    Sai kisamu mazubi inda zaki hada kayan hadin ki zakisa gyadarki amma gasashshe ko peanut butter ko soyayyar gyada ni nayi amfani da gasashsheya na dakashi amma sama sama

  4. 4

    Nasa mishi dandano,yajin soya da ruwa kadan na kwabashi acikin yajina akwai tafarnuwa,chitta,kananfari da sauransu

  5. 5

    Sai ki shafawa namanki kimayar dashi oven yakasu na mintuna 5 zuwa 6 sai ki Kara fiddoshi ki kara shafa mishi kayan hadinki ki mayar dashi oven haka zaki tayi har Kayan hadinki yakare sannan kuma kinga naman naki ya gasu yazama kilishi shikenan agwada lfy

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Sumy's delicious
Sumy's delicious @cook_13830250
rannar
Gombe State, JikadaFari

Similar Recipes