Jallof din shinkafa da spicy yam

Abincin Nan yayi Dadi sosai kannena na girkawa har tambaya ta suke ko fried rice ce😁doyar kuwa cewa sukai wacce duniyar ce wannan 😋
Jallof din shinkafa da spicy yam
Abincin Nan yayi Dadi sosai kannena na girkawa har tambaya ta suke ko fried rice ce😁doyar kuwa cewa sukai wacce duniyar ce wannan 😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na daura ruwa a wuta ya tafasa sai na jajjaga attaruhu da albasa da tafarnuwa na yanka su karas da koren wake sai na juye ruwan zafin a babbar roba na mayar da tukunyar Kan wuta sai na zuba Mai da yai zafi na kawo jajjagen na zuba na soya su sama2 na tsaida ruwa sai na wanke shinkafar da ruwan dumi da gishiri. Na zuba a tafashen ruwan zafi na zuba su dandano curry da onga tare da peas na rufe bayan kamar minti 10 na zuba karas da koren wake na rage wutar sosai har ta tsotse.
- 2
Na fere doya na yanka ta sirara kamar yankan Dan yatsa sai na wanke na zuba Dan gishiri da Jan onga sachet daya
- 3
Na jujjuya na daura Mai a frying pan da yayi zafi na zuba doyar
- 4
Sai na barta ta soyu na kashe na jajjaga attaruhu da albasa da tafarnuwa na yanka albasa da cabbage na zuba Mai dan kadan a frying pan na zuba jajjagen na soya sai kawo yankakkiyar albasa na zuba bayan minti 2 na zuba cabbage da dandano na cigaba da juya sai na kawo doyar na zuba akan hadin na juya su har suka hade ajikin doyar. Za'a iya ci haka ko da duk abun da mutum yaso
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai