Crispy Kaza
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki wanke kazar kitsaneta saiki aje gefe
- 2
Markada albasa da tafarnuwa da Danyen citta masoro saiki juye akan Danyen kazar ki cakudata ko ina yasamu saiki zuba maggi ukku da gishiri kisake jujjuyawa kisata a firij da dare yakwana acikin mazubi rufeffe
- 3
Tankade fulawa kirabata biyu na farkon kisaka maggi daya da gishiri da masoro da qwai ukku da garin barkono saiki zuba Mata ruwa kikwabata Kamar kaurin kunu
- 4
Dayan fulawar kuma haka zaki barta a garinta kisaka Mata maggi daya
- 5
Kidaura mai akan wuta yayi zafi saiki fitoda kazarki daga firij
- 6
Kidauki yankar kaza guda daya kitsomata a kwababbiyar fulawa me qwai saiki dagota tadige saiki sanya a dayan garin fulawar kijujjuya yazamo ko ina yaqame saiki sanya a mai me zafi zaiyita soyuwa ahankali inyayi ruwan qasa saiki juya inyasoyu saiki tsame
- 7
Haka zakiyi wa sauran kazar dukka, hmmmmmmm dadinta bazaki baiwa yaro me qiwaba😜
- 8
Aci dadi lfy
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai (6)