Dambun cous-cous

Ina matuƙar son dambu musamman na kuskus😋
Dambun cous-cous
Ina matuƙar son dambu musamman na kuskus😋
Umarnin dafa abinci
- 1
YADDA AKE HAƊAWA*
_Da farko za ki gyara alayyahun ki ki yanka su manya ki zuba gishiri ki zuba ruwa ya ɗan yi mintuna sai ki wanke ki tsane shi ki ajiye a gefe.
- 2
Sannan ki jajjaga taruhun ki da albasa dai dai yadda kike son ta fito miki ki daka gyaɗar ki, ki nemi roba mein kyau ki juye kuskus ɗinki
- 3
Sannan ki zuba gyaɗa da kayan miyanki da su curry ki gauraya sai ki ɗauko alayyahun ki ku zuba dama kin silala namanki kin yanka shi ƙanana sai ki juye ki juye albasarki da ɗan dama wanda kika yanka sai ki ɗauko ruwan namanki ki juye a ciki iya shi ya isa ya turara miki ki gauraya har sai ya haɗe jikinsa sannan ki juye a madambacin ki mai kyau ki ɗaura a kan wuta, ki bashi mintuna za kiji yana fitar da ƙamshi sosai sai ki sauƙi ki zuba masa mangyaɗan ki da kika soya in kina so za ki iya zubaƙuli
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai