Pizza ta dankali

Fulanys_kitchen
Fulanys_kitchen @cook_14365493
sallari qts Kano

Abun baa magana

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Dankalin turawa
  2. Cheese
  3. Albasa
  4. Ataruhu
  5. Kwai
  6. Mai
  7. Maggi
  8. Tafashshen nama

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaki samu dankalin ki lafiyayye ki fere shi ki yankashi ki wanke se ki tsane a colenda se ki dora man gyada a wuta ki yanka albasa ya soyu sosai se ki zuba gishiri dan kadan a cikin dankalin ki juya ya shafu a ko ina se ki zuba a cikin mai ki soya,bayan ya soyu se ki tsaneshi.

  2. 2

    Se ki kawo albasa ki bareta ki yankata round,ki jajjaga ataruhun ki ba me yawa ba,ki kawo tafashashshen naman ki ki yanka shi kanana sosai,ki hada maggin ki waje daya,ki dakko cheese dinki ki kankarashi a abun kankara kubewa me dan yawa,ki fasa kwan ki ki kadashi kisa maggi,albasa,curry,ataruhu da siga dan kadan,

  3. 3

    Se ki kawo soyayyen dankalin ki ki zuba shi a cikin kwai ki juya sosae,se ki dakko kaskon da zaki soya ki zuba man gyada kamar zaki soya kwai idan ya danyi zafi se juye kwai da dankalin a ciki,

  4. 4

    Se ki dakko cheese ki dan barbada a saman ki kawo naman ki ki zuba shima ki jera albasar da kika yanka a kai se ki kawo sauran cheese din ki zuba a kae se kisa murfi ki rufe,kar kisa wuta da yawa hakan ze bashi damar soyuwa a tsanake ki bashi kamar minti biyar zuwa bakwai daga haka zakiga cheese dinki ya narke dankalin ya kumburo kiji kanshi ya cika miki kitchen,

  5. 5

    Daga nan se ki kashe wutar ki,kisa chokali me fadi ki dago shi a hankali kisa a faranti,ki tafi kina taku daidai ki kaiwa me gida,hajiya ranar inaji se dae yace ga mukullin motata na baki kyauta❤️

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fulanys_kitchen
Fulanys_kitchen @cook_14365493
on
sallari qts Kano

Comments

Fatima Taheer
Fatima Taheer @cook_19946080
Ina datambaya komai guri daya zahada sai azuba a pan a soya

Similar Recipes