Share

Ingredients

  1. Fulawa
  2. Kabeji
  3. Karas
  4. Albasa
  5. Maggi
  6. Ruwa

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko wadannan abubuwan zaki buqata

  2. 2

    Sai ki wanke kabeji, albasa da karas, sai ki yanka kabejin ki sirara da albasa Amma albasa bada yawa zaki sa ba sai ki goge Karas din ki

  3. 3

    Sai ki dora su akan wuta ki saka maggi Kagan, amma wutar a qasa zaki sa, ba sai kin sa ruwa wurin dahuwar Su ba, Kawai ki saka wutar a qasa, ki b arshi yayi kamar minti goma sai ki sauke

  4. 4

    Sai ki dauko fulawar ki, ki samata maggi ki kwaba ta ruwa, kwabin ruwa ruwa zakiyi shi ya dan fi na fanke ruwa, Sannan zakiyi amfani da brush wurin shafa shi

  5. 5

    Sai ki saka non stick pan din ki a wuta, ki shafa fulawar akai yayi round shape.

  6. 6

    Toh da yayi zaki ga gefen ya fara dagowa sai kisa hannu ki cire ki ajiye.

  7. 7

    Sai dauko falefalen fulawar ki samata hadin kabejin a farko

  8. 8

    Sai ki murna, Sannan Ki nado gefen da gefen, Idan kin nado sai kici gaba da murdawa, kafin kizo qarshe sai ki kwaba fulawa mai kauri ki shafa a qarshen sai ki nade

  9. 9

    Toh sai ki daura man ki a wuta yayi zafi sai ki soya har yayi golden brown.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ayshas Treats
Ayshas Treats @ayshas_Treats1
on
Kano
I love cooking and it's my hobby
Read more

Similar Recipes